1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kara wa'adin dokar ta-baci a jihar Diffa.

Abdoulaye Mamane AmadouMay 27, 2015

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da tsawaita dokar ta-baci ta tsawon watanni uku a yankin jihar Diffa mai fama da matsalolin 'yan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1FX9z
Amadou Salifou
Amadou SalifouHoto: DW/M. Kanta

'Yan majalisar dai sun tabka mahawara mai zafin gaske dangane da halin da jamaa suke ciki a yankin na Diffa musamman ma batun daukar nauyin jamaar da aka kwaso daga yankunan na Tafkin Chadi wadanda aka kiyasta yawansu sama da mutun dubu 20, kuma 'yan adawar suka ce baa basu kyawawar kulawa ba, da kuma batun baiwa sojojin kayayakin aiki da ya haifar da cece kuce a fannoni daban-daban na kasar ta Nijar. To amma duk da hakan 'yan majalisar sun aminta da sake fadada dokar ne da kuriu 88 kamar yadda dan majalisa Saidou Bakari Sangare na jamiyyar Lumana Afirka ya yi tsokaci a kai...

'Yan majalisu na adawa sun nemi a kawo gyara.

Bakari Saidou
Bakari SaidouHoto: DW/M. Kanta

"Dokar dole ne mu amince da ita, domin abin da ya shafi kasa dole ne 'yan kasa su yadda da shi, amma kamar yadda muka fadi ne duk wani abu na kasa idan ya shafi kishin kasa zamu kamawa gwamnati, to don haka ne muka jefa kuriar amincewa sai dai akwai matsalolin da ya kamata a tsaya a yi gyaransu kamar mutanen da aka koro daga Tsibirin Karamga, da kuma batun kayan aikin sojoji."

Duk da hakan dai wasu yan majalisun da suka aminta da dokar sun ce sojan kasar ta Nijar sun nuna jarumtaka game da yakin da suke duk kuwa da matsalolin da ake cewa suna fiskanta, kamar yadda Honorable Saidou Amma dan majalisar dokoki na jamiyyar CDS Rahama mai goyon bayan gwamnati ya yi bayani...

Sojojin Nijar a Diffa
Sojojin Nijar a DiffaHoto: Desmazes/AFP/Getty Images

'Yan majalisa sun yaba kokarin sojojin Nijar.


"Kowa yasan sojojin Nijar sun yi abin azo a gani a bakin iyaka saboda sun kora sau daya, sun kora sau biyu sun kora sau uku sun buga sau hudu, sau biyar to duk dama makashin maza, maza ka kashe shi kamar yadda ake cewa, sabili da haka ne dokar zata taimaka wa sojojin cikin ayyukansu na samar da tsaro a yankin."


Hukumomin na Nijar sun ce dokar ta-bacin tayi wani babban tasiri a jihar ta Diffa ganin yadda hare-haren na yan Boko Haram suka ragu, sannan rayuwar mazauna jihar ta sake kankama a cikin walwala sakamakon ayyukan da jamian tsaro ke yi. a jawabin da ya yi a gaban yan majalisun, Ministan cikin gidan kasar ta Nijar Hassoumi Massaoudou ya tabbatar cewa binciken da jamian tsaron ke yi ya basu damar kama mutane sama da dari shidda wadanda ko dai 'yan Boko Haram ne, ko kuma suna da alaka dasu.