An kammala taron AU karo na 25
June 15, 2015Wannan ne karo na 25 na taron wanda ke samun halartar kasashe sama da 50 na nahiyar, kuma taken bana shi ne tallafawa mata da kuma samar da cigaba dan cimma muradun Afirka a shekara ta 2063.
Lokacin da ta bude taron shugabar majalisar zartarwar Kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma ta yaba da irin matakan da nahiyar ta dauka wajen dakile annobar Ebola a yankin Yammacin Afirka, kuma ta ce a yanzu haka, abin da ya kamata su sanya a gaba shi ne tallafawa mata da yara musamman wadanda ke yankunan da ke fama da rikici, a kuma samar da tsaro, domin nahiyar ta koma cikin wani yanayi na kwanciyar hankali.
Ta ce: "Abun takaicin shi ne mata da yara ne yaki ya fi shafa, wadanda ma basu taba sanya baki a wani abin da zai janyo yaki ba. Matakin da muka dauka na dakile yaki yanzu, ya kamata ya baiwa mata da yaran da suka wahala a hannun Boko Haram ko Alshabab, sabon fata, kuma wannan ya kamata ya shafi duk wadanda ke rayuwa a yankunan da ke fama da rikici."
Da ma kamata ya yi taron ya tattauna abubuwa da dama musamman muradun kungiyar na shekara ta 2063, da rikicin siyasar Burundi da ma tayin da ake yi na kasuwanci mara shinge tsakanain kasashen da kuma hanyoyin samar da kudaden da zasu tafiyar da rundunar Afirkan da kungiyar ke kokarin ganin ta samar.
Sai dai labari ya sauya bayan da wani alkalin kotu a Afirka Ta Kudun ya hana shugaba Omar al-Bashir na Sudan barin kasar, da hujjar cewa akwai samancin kasa da kasa da kotun ICC ta bayar tun a shekara ta 2009, inda take zarginsa da aikata miyagun laifuka a yankin Dafur, a wani abin da ke kara zurfafa takaddamar da ke tsakanin Afirka da kasashen yamma, inda suke zargin kotun ICC, na hukunta manyan laifukan yaki da tuhumar kasashen Afirka kadai.
Amma, tun kafin ma kotun ta yanke hukunci, ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Al-Ghandour ya ce an gayyace su taron ne kuma da zarar lokaci ya yi za su koma:
Ya ce: "Mu baki ne a wajen gwamnatin Afirka Ta Kudu mai masaukin baki, kuma na yi imanin cewa gwamnatin Afirka ta Kudun za ta iya dakatar da koma waye ke kokarin hana shugaba Bashir barin kasar nan, kuma ina tabbatar muku cewa Bashir zai bar kasar nan a kan lokaci".
Wannan tabbaci da ya ba da ne ma aka gani, inda jim kadan bayan kammala taron masu aiko da rahotanni suka tabbatar cewa jirgin da shuaga al Bashir ya zo da shi, ya kama hanyar gida wato Khartoum.
Wani abu kuma da ya dauki hankali a taron shi ne jawabin da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya yi, inda ya zargi Birtaniya da kokarin ci da gumin Afirka ta wurin anshe mata arzikin karkashin kasa ko ta halin kaka
Ya ce: Suna so su anshe mana manmu da lu'u Lu'unmu da zinarinmu da duk wani arziki da muke da shi a karkashin kasa, a tunaninsu dan me wadannan 'yan kauyen za su mallaki duk wannan? musamman idan Birtaniya ta duba tsibiranta ta ga ba komai sai kwal. Su kansu Amirka, duk da fadin kasa da jiragen sama da na kasa da suke da suna fargabar cewa man zai kare saboda haka akwai saura a Afirka wanda ba su ma san abin da za su yi da shi ba dan haka mu je can mu raba su da shi ko ta halin kaka.
Bayan kammala wannan taro, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban KI-Moon ya gana da manema labarai, inda ya nuna bacin ransa da yadda ba a kai ga kama al- Bashir ba kuma ya nuna goyon bayansa na cewa lallai ya kamata a aiwatar da kudurin kotun na ICC.