An kama wanda ya kitsa juyin mulki a Saliyo
December 6, 2023Hukumomi a kasar Saliyo sun samu nasarar cafke wani jigo daga cikin wadanda suka kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba, tare da wasu mutane biyu da ke taimaka masa, adadin da ya kai mutane 60 kenan da aka kama zuwa yanzu bisa zargi da hannun a yunkurin juyin mulkin.
Karin bayani:An kama wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulki a Saliyo
Ministan yada labaran kasar Chernor Bah, ya ce sun kama Amadu Koita, tsohon soja kuma dogarin tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, wanda ya yi fice a shafukan sada zumunta wajen sukar lamirin gwamnatin shugaba mai ci Julius Maada Bio.
Wani jawabi da mataimakin ministan yada labaran kasar Yusuf Keketoma Sandi ya gabatar a gidan rediyon kasar, ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai sojoji 37, da fararen hula 10, sai wasu korarrun sojoji guda 4 da 'yan sanda 5 da kuma wani 'dan sanda daya da ya yi ritaya.
Karin bayani:An bude wuta a gidan yarin Saliyo
Yunkurin juyin mulkin na ranar 26 ga watan Nuwamban da ya gabata ya janyo asarar rayukan mutane 21.