1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama Magungunna na jabu zuwa Afirka

September 22, 2014

Hukumar Kwastam ta duniya OMD, ta sanar da kama magungunna na jabu milyan 113 zuwa Afirka, a wani bincike da jami'an kwastan suka gudanar

https://p.dw.com/p/1DGww
Hoto: Fotolia/Nenov Brothers

Binciken dai an gudanar da shi ne, daga karshen watan Mayu zuwa farkon wajan Yuni da suka gabata, wanda kuma ya shafi kasashe 14 na Afirka. An samu wannan adadi na magungunnan na jabu a binciken kwanaki goma kawai, inda aka samu magunguna masu hadarin gaske musamman a tashoshin ruwan kasashen Jamhuriyar Benin, da Tanzaniya, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo kuma mafi yawan magungunan sun fito ne daga kasashen China, da kuma Indiya a cewar hukumar Kwastam din ta Duniya, kuma a wannan karo har da magungunna na dabbobi allurai fiye da dubu 100.

Hukumar ta yi kira ga hukumomin kasashe da su tashi tsaye wajan kare lafiyar al'ummomin su daga wannan barazana ta muyagun mutane masu neman kudi ta hanyar nakkasa wasu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo