SiyasaJamus
An kama daruruwan bakin haure a Libiya
October 3, 2021Talla
Masu gadin teku a Libiya, sun kama wani jirgin ruwan katako shake da bakin haure kimanin 500 wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa Turai.
Wannan shi ne kame na baya-bayan nan da aka yi na wasu da ke barin kasashensu na asali musamman Afirka domin shiga nahiyar Turai ala kulli halin.
Kamen ya faru ne kwanaki biyu bayan wani farmaki da jami'ai suka kai kan wasu bakin hauren akalla dubu hudu a yammacin kasar ta Libiya.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, UNHCR, ta ce an jibge bakin hauren da aka kama ranar Lahadi a wata matatar mai da ke a birnin Zawiya na kasar.
Kasar ta Libiya dai ta kasance wata cibiya da gallibin 'yan Afirka masu neman rayuwa a kasashen yamma ke bi domin shiga ta barauniyar hanya.