An kai wasu jerin hare-hare a birnin Maiduguri
October 14, 2015Talla
Rahotanni da ke fitowa daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na cewa wasu sabin harin Bama-Bamai da aka kai a daren jiya a wurare uku da ke unguwar Sajeri, sun hallaka mutane da dama tare da jikkata wasu. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan wadanda ake zaton ‘yan Kungiyar Boko haram ne sun tada bama-bamai da ke daure a jikin su a wasu wuraran da jama’a ke taruwa. Saidun sun tabbatar cewa, a wannan karon wasu maza ne suka kai wadan nan hare-hare na kunar bakin wake saidai babu wanda ya iya tantance daga inda suka fito.