An kai harin kunar bakin wake masallacin juma'a na Maiduguri.
July 13, 2012A Najeriya wani dan kunar bakin wake ya kai hari wanda ya hallaka mutane biyar yayin da suke fitowa daga babban masallacin juma'a na Maiduguri dake kusa da fadar Shehu Borno bayan kammala sallar juma'a. Rahotanni sun ce mataimakin gwamnan jihar Borno Zanna Umar Mustapha da Shehun Borno Umar Garba el- Kanem da kuma wani babban malamin addinin musulunci sun tsallake rijiya da baya a wannan hari. An baiyana cewa dan kunar bakin waken yaro ne karami dan kimanin shekaru 15 da haihuwa. kakakin rundunar tsaro ta Soji a jihar Borno Kanar Sagir Musa yace akalla mutane shida sun sami raunuka. Babu dai wanda ya dauki alhakin kai wannan hari sai dai a Najeriyar hare hare makamancin wannan da kungiyar Ahlul Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram take kaiwa ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da dama.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi