An kai harin kunar bakin wake kusa da Maiduguri
June 28, 2015Akalla mutane biyar sun rasu wasu kuma goma sun ji rauni sakamakon wani bam da ke jikin daya daga ciki 'yan kunar bakin waken guda uku ya tashi a unguwar Amole da ke gefen birnin Maiduguri a Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. A cewar 'yan kungiyar agajin gaggawa na jihar ta Maiduguri, harin ya wakana ne tun a yammacin ranar Asabar kuma shaidun gani da ido sun ce 'yan kunar bakin waken su uku ne yayin da wata mota mai kirar SUV ta saukesu. Sun yi kokarin shiga cikin asibiti amma kuma suka lura cewar akwai tsaro, inda daya daga cikinsu ya tayar da nashi bam yayin da sauran suka tsere.
A ranar ta Asabar din ce kuma wasu 'yan mata biyu suka yi yunkurin kai wani harin kunar bakin wake a garin Jakarna da ke da nisan kilometa 40 da birnin na Maiduguri, amma kuma Allah bai basu sa'a ba. Sai dai 'yan matan biyu sun hallaka kansu bayan da bam din daya daga cikinsu ya tashi yayin da suke jiran motar da za su shiga.