An kai harin kunar bakin wake a Mogadishu
August 8, 2020Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu a wannan Asabar yayin da gwammai kuma suka jikkata a Mogadishu, lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta fashe a wani sansanin soji da ke babban birnin Somaliya. Babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai wannan hari da ya afku a kusa da filin wasa na kasa.Sai dai hukumomi sun saba alakanta irin wadannan hare-hare da 'yan tayar da kayar baya na al-Shabaab, wadanda ke aiwatar da yaki irin na sunkuru a Somaliya tun shekarar 2008.
Shaidu sun tabbatar wa kanfanin dillanci labaran Faransa na AFP cewa, motar da ke cike da abubuwan fashewa ta wuce shingen farko kafin ta tarwatse a kusa da sansanin. Hare-haren bama-bmai dai sun zama ruwan dare a Mogadishu, ko da yake sun ragu ainun tun daga farkon wannan shekarar i zuwa yanzu.