An kafa gwamnatin rikon kwarya a Libiya
February 5, 2021Talla
An dai zabi Muhammad Yunus Al-manfy a matsayin Shugaban majalisar zartarwa na gwamnatin rikon kwaryar yayin da aka zabi Abdulhameed Dabeebah a matsayin sabon firanminista.
Wannan zaben dai ya kawo karshen mulkin tsofin jami'an gwamnatin hadakar kasar da ta kunshi Aqilah Saleh, shugaban majalisar Gabashin kasar, da Fathy Bashaga, ministan cikin gidan gwamnatin Tripoli wadanda suka sha kaye a zaben.