1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta ɓace a ƙasar Phillipines

Yahouza SadissouFebruary 24, 2006

A sakamakon yunƙurin juyin mulki shugabar ƙasar Phillipines ta kafa dokar ta ɓace.

https://p.dw.com/p/Bu1U
Hoto: AP

Shugabar ƙasar Phillipines Gloria Aroyo, ta kafa dokar ta bace a faɗin ƙasar baki ɗaya, a sakamakon yunƙurin juyin mulki, da wasu sojoji su ka shirya domin kifar da ita.

A duk tsawon makon da damu ke ciki, an ta yi jita jitan shirya wannan juyi mulki, a yayin da al´ummmar ƙasar ke tunni da cikwan shekaru 10, da hambarra da shugaban yan mulkin kama karya Ferdinand Markos.

A ciki jawabin da ta yi, ta kafofin sadarwa shugabar ta bayyana wa al´umma dalilan kafa wannna doka, ta kuma umurci jami´an tsaro masu biyyaya ga gwamnati su ɗauki mattakan da su ka wajabta, don maido doka da oda a cikin kasa.

Ya zuwa yanzu, an kama Janar Danilo Lim, shugaban rundunar ƙundumballa ta ƙasa, da kalan Ariel Quevedo.

Kazalika, a na tsare da shugaban rundunar yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike, domin capke duk, wanda a ka samu da hannu, a cikin wannan yunƙuri, inji shugaba Arroyo.

A sakamakon wannan saban rikici, da ke shirin ɓarkewa a ƙasar, hukumomin yan sanda sun janye izinin da su ka bada, na shirya tarruraka a wani dandali mai tarihi, da ke Manillles, babban birnin ƙasar ,wanda a harabar sa ne, al´ummomin Phillipines, su ka hitto mazan su, da mata, a shekara ta 1986, domin shirya zangar da ta zama sanadiyar kiffar da tsofan shugaban mulkin kama karya Ferdinand Markos, da kuma tsofan shugaba Joseph Estrada, wanda aka kora daga mulki, a shekara ta 2001.

Saidai duk da wannan haramci, a kalla mutane dubu daya sun halarci wurin taron gangamin.

Sun bukaci shirya zanga zangar ta yau, domin nuna ƙin jinnin shugabar ƙasa Gloria Arroyo.

Binciken da rundunar soja ta gudanar, ya shaida cewar burjinanun sojojin,sun bukaci anfani da wannan taro, domin bayyana wa jama´a matakin da su ka ɗauka, na tawaye ga mahunkunta.

A tsawan shekaru 20 da su ka gabata, ƙasar Phillipines ta fuskanci juyin mulki kokuma yunkurin juyin juyin mulki fiye da 10.

Amma a wannan karro masharahanta na hasashen cewar , bisa dukan alamu,shugaba Arroyo ce ta kirkiro wannan yunkurin hambaren da ita, domin haskaka tarmuamuwar ta, da a halin yanzu ta fara dushewa, ta kuma anfani da wannan dama domin tuɓe sojojin da ta azawa karan tsana.