Sabon shugaban Somliya ya dauki madafun iko
June 9, 2022Talla
An kaddamar da sabon shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud wanda lokacin jawabi ya bukaci kasashen duniya su kara taimakon kasar magance matsaloli da suka hada da fari gami da tsaro.
Shi dai Hassan Sheikh Mohamud ya rike madafun iko daga shekara ta 2012 zuwa 2017 kafin ya sake dawowa ya lashe zaben da ya gabata.
Ita dai kasar Somaliya ta kwashe fiye da shekaru 30 cikin rikice-rikice na siyasa da yakin basasa da hargitsi masu ikirarin jihadi na kungiyar al-Shabaab.