Najeriya ta kaddamar da sabbin takardun Naira
November 23, 2022Gabatar da sabbin takardun na Naira dubu da Naira 500 da kuma Naira 200 da aka sake wa fasali a Najeriyar muhimmin mataki ne a kokari na nemo bankin zaren tattalin arzikin kasar da yake kara shiga mawuyacin hali musamman darajar Naira. Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ne dai ya kaddammar da sabbin takardun kudin a Abuja, wanda ya bayyana dalili da ma muhimmancin yin hakan.
‘'Ana sake yanayin takardar kudi ne don cimma muhimman manufofi da suka hada da kyautata tsaron takardaun kudi, magance yin jabun kudi da rage tsadar kula da takardun kudin na Naira, don haka akwai bukatar samun kula da kudade da ke kai kawo a tsakanin al'umma da magance ‘yan baranda masu boye takardun kudi. Shi yasa na bada amincewa a buga sabbin takardun kudin, a bisa wannan ne na amince da bada izinin sake fasalin takardun kudin na Naira 200 da 500 da Naira 1000 daya''.
Sabbin takardun kudin dai kalarsu ne aka canza ba wai hotuna ko rubutun da ke jikinsu ba, domin hatta rubutun ajami na nan ba'a canza su ba, Naira 200 da a da take da ruwan hoda yanzu ta koma mai launin kore, yayin da tsohuwar Naira 500 ta koma launin Naira 200 ta da can , sai tsohuwar Naira dubu daya da ke da launin ruwan kasa a yanzu ta koma shudiyya.
Tuni masana harkokin tattalin arziki ke bayyana alfanun da ke tattare da buga sabbin takardun kudin. A bisa dokar aiki ta babban bankin Najeriya ta 2007, an baiwa bankin izinin sake fasalin takardar kudi a kowane shekaru 5 zuwa takwas, inda yanzu shekaru 20 kenan rabon da a yi wannan, abin da ya sanya gwamnan babban bankin Godwin Emefiele bayyana cewa.
‘'Amfani da ke tattare da sake fasalin takardun kudin Naira ga tattalin arzikin Najeriya na da yawa domin zai taimaka shawo kan hauhawan farashin kayayyaki domin zai sanya a maido da kudadden da aka boye zuwa babban bankin Najeriya, wannan zai taimaka tsara manufofin tattalin arziki , haka nan zai taimaka manufara rage amfani da takardar kudi wajen kasuwanci a tsarin amfani da katin banki. Zai taimaka rage cin hanci da rashawa domin za'a sa ido a kan manyana takardun kudi da ake amfani da su wajen cin hanci, ta yadda hukumomin yaki da cin hanci da rashawa zasu iya sanya ido a kan kai da komowar kudadden'' .
Babban bakin Najeriyar dai ya ce tun daga lokacin da aka sanar da sauya takardun kudin an fara ganin nasara, domin an ga karuwa ta yawan kudadden da ke kai kawo zuwa sama da Naira triliyan biyar a kasar. Najeriya dai na cikin kasashen Afrika 4 da ke buga kudinsa a cikin kasar daga cikin kasashe 54 da ake da su a nahiyar.