An jingine bayyana sakamakon zaben Zambiya
January 21, 2015Hukumar zaben kasar Zambiya ta jangine bayyana sakamakon zabe saboda korafin da 'yan adawa suka gabatar, bayan 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye kan magoya bayan 'yan adawa.
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Zambiya ya nuna dan takaran jam'iyya mai mulki ta PF, Edgar Lungu dan shekaru 58 kana ministan tsaro da sharia ke kan gaba da jagoran 'yan adawa Hakainde Hichilema dan shekaru 52 masanin tattalin arziki na jam'iyyar adawa ta UPND.
Mahukuntan kasar sun tura jiragen sama masu saukan ungulu domin dauko akwatunan zabe. kasar tana da kimanin masu zaben milyan biyar daga cikin al'umar kasar milyan 15. Karkashin dokokin kasar ta Zambiya duk wanda ya samu nasara zai kammala wa'adin mulki Marigayi Shugaba Michael Sata wanda ya rasu kan madafun iko a watan Oktoba, inda za a sake zaben gama gari a shekara mai zuwa. Shugaban wucin gadi Guy Scott baya cikin 'yan takara.