An janye zargi da ake wa shugaban kasar Kenya
December 5, 2014Babban mai shigar da kara a kotun da ke hukunta masu manyan laifuka ta duniya, ICC, ta bayyana janye caje-caje da ake wa Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a wannan Jumma'a, bisa zarginsa da hannu a cin zarafin al'umma, inda ta ce matsalar ita ce kotun na gurfanar da manyan masu rike da madafun iko a gabanta saboda wasu laifuka na take hakkin dan Adam.
Florence Olara mai magana da yawun ofishin mai gabatar da karar ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa Fatou Bensouda mai gabatar da karar a wannan kotun kasa da kasa ta gabatar da takardun janye caje-caje da ake wa Shugaba Uhuru Kenyatta.
Shugaba Kenyatta dai ana zarginsa da hannu a wasu ayyukan take hakkin dan Adam da suka hadar da aikata kisa da fyade da tilastawa mutane gudun hijira a rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar Kenya a shekara ta 2007 da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane dubu daya.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo