1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbi tsohon firaministan Pakistan

November 3, 2022

Tsohon firaministan Pakistan da magoya bayansa sun gamu da tashin hakalin ne a yanki Wazirabad da ke lardin Punjab, an kuma garzaya da shi zuwa asibiti.

https://p.dw.com/p/4J0ws
Toshon fimanistan Pakistan, Imran Khan a filin gwagwarmaya
Hoto: Arif Ali/AFP/Getty Images

Rahotannin da ke fitowa daga Pakistan na cewa wani dan bindiga ya bude wuta kan ayarin tsohon firaministan kasar Imran Khan lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Islamabab domin kaddamar da wani gangamin matsa wa gwamnati lamba.

Shaidu sun ce maharin ya ji wa Imran Khan rauni a kafa sai dai ba mai tsanani ba, sannan akwai wasu da dama daga cikin magoya bayansa da suka ji raunuka.

Shi dai tsohon fimanistan na Pakistan da ayarin magoya bayansa ya gamu da wannan tashin hankali ne a gundumar Wazirabad da ke cikin lardin Punjab, kuma tuni aka kai shi asibiti da ke a birnin Lahore.

Manufar gangamin da suka tsara dai, ita ce ta neman gwamnatin kasar ta shirya zabe gabanin wa'adi.

Tun bayan tumbuke shi da aka yi daga mukamin firaminista ta hanyar kuri'ar yankan kauna a Pakistan ne dai, Imran Khan ke ta zargin wanda ya gaje shi, Shahbaz Sharif da shirya masa makarkashiya.

Haka ma ya dora alhakin tumbuke shin a kan gwamnatin kasar Amirka.