1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Adawa da sojojin Faransa

November 22, 2021

Faransa ta bukaci kawo karshen takaddamar da ta barke a karshen makon da ya gabata, bayan da matasan kasar Burkina Faso suka dakatar da dakurunta da ke kan hanyarsu ta zuwa Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/43L3C
Burkina Faso Blockade Frankreich Militär
MAsu zanga-zanga a Burkina faso, sun hana sojojin Faransa shiga Jamhuriyar NijarHoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

Masu zanga-zangar dai na nuna adawa da rawar da tsohuwar kasar da ta yi wa Burkina Fason mulkin mallaka, za ta taka a yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel. Daruruwan masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin birin Kaya, birni na biyar mafi girma a kasar Burkina Faso da ke yammacin nahiyar Afirka. Da dama dai na ganin Faransa na kokarin shiga sharo ne ba shanu ga rikicin da kasar ta kwashe tsawon shekaru biyar ta na fuskanta, inda suke nuna adawa da dakarun da Faransan ta tura yankin domin yaki da kungiyoyin masu gwagwarmaya da makamai.

Karin Bayani: Hana hawa babura saboda tsaro a Burkina Faso

Arangamar ta karshen makon da ya gabata dai, ta samo asali ne bayan da masu zanga-zangar suka ki yarda ayarin dakarun Faransa su shiga kasar ba tare da sun ga ababen da suke dauke da su a motocinsu ba, suna masu zargin Faransa da yiwuwar samar wa 'yan ta'addan makamai. A ranar Asabar din da ta gabata lamarin ya kazanta, bayan da masu zanga-zangar suka yi yunkurin matsawa kusa da dakarun. Matakin dai ya sanya sojojin sun bude musu wuta, tare da harbin mutane hudu.
Tun daga watan Yulin da ya gabata ne dai, ake gudanar da jerin zanga-zanga a kasar ta Burkina Faso saboda matsalar tsaro da ke kamari. A cewar kakakin rundunar sojojin Faransar Pascal Lanni an dauki matakin matsawa da dakarun zuwa kudancin kasar, domin rage fargaba da kuma kaucewa sake arangama tsakaninsu da matasan masu zanga-zanga. Ya kuma yi kira kan watsi da labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta da ke nuni da cewa dakarun sun yi harbin kan mai uwa da wabi, yana mai cewa manufarsu ita ce yaki da 'yan ta'adda da kuma tabbatar da tsaron 'yan kasa ba akasin hakan ba.

Symbolbild | Amnesty: Kinder leiden unter Terror in Westafrika
Matsalar tsaro ta tilastawa al'ummar Burkina Faso da dama yin gudun hijiraHoto: imago images/Joerg Boethling

Karin Bayani: Yunkurin samar da tsaro a wasu kasashen Sahel

A nasa martanin kan zanga-zangar, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce kasashe biyar a yankin Sahel da suka hada da Mali da Burkina Faso da Nijar da Chadi da kuma Mauritaniya, sun nemi taimakon Faransa a yakin da suke yi da ta'addanci. Faransa dai na yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin tun a shekarar 2013, sai dai ta na duba yiwuwar rage yawan dakarunta daga fiye da 5,000 zuwa 3,000 a daidai lokacin da kasar da ta yi mulkin mallaka ke shan mumunar suka kan kasancewarta a kasashen Mali da Burkina Faso.