Gbagbo zai ci gaba da zama a gidan yari
January 18, 2019Talla
Kotun ICC ta wanke Gbagbo da Charles Blé Goudé a ranar Talata da ta gabata, amma yanzu za su ci gaba da kasancewa a gidan kurku har zuwa daya ga watan Faibreru, bayan da alkalin alkalai na kotun ICC ya daukaka kara.Gbagbo wanda ake tsare da shi kusan shekaru bakwai a birnin Hague, an yi masa sharia'a ne kan laifuka na take hakkin dan Adama a tarzomar da ta biyo bayan zaben kasar na shekarun 2010 zuwa 2011 inda mutum sama da dubu uku suka rasa rayukansu.