An fatattaki Boko Haram daga Maiduguri
February 1, 2015Rahotannin da ke fitowa daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na nuna an cewa kura ta fara lafawa a fafatawar da aka yi tsakanin ‘yan Kungitar Boko Haram da ke neman shiga garin da kuma rundunar sojojin Najeriya da ke kokarin dakile shiga don karbe iko da birnin. Tun da sanyin safiyar wannan Lahadi al'ummar garin Maiduguri suka wayi garin da jin karajin harbe-harbe da fashewar abubuwa masu karfi da ake zaton bama-Bamai ne a Molai da ke hanyar Damboa da kuma Muna hanyar Mafa. Babu alkaluma na wadanda abin ya ritsa da su ya zuwa yanzu.
Wasu rahotanni sun nuna cewa wani bam ya fashe a kofar gidan wani dan siyasa garin Potiskum a jihar Yobe inda ake fargaba mutane bakwai sun mutu, wasu da dama kuma sun jikata.
A ‘yan kwanakin nan dai ana fafatawa tsakanin ‘yan bindiga da kuma jami'an tsaro na kasahsne Cadi da Kamaru inda bayanai da ba na hukumomi ba ke cewa an samu nasarar karbo garuruwan Gamboru da kuma wasu kauyuka kusa da wannan yanki.