An fara shari’ar wasu ’yan tsatsauran ra’yin islama na ƙasar Holland a birnin Amsterdam.
October 16, 2006Yau ne, a birnin Amsterdam na ƙasar Holland, aka buɗe shari’ar wani ɗan ƙasar mai asali daga Marokko, wanda ake zargi da kasancewa ɗan wata ƙungiyar ’yan ta’adda masu bin tsatsauran ra’ayin islama, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma shirya kai hare-hare kan ’yan siyasan ƙasar. Jami’an hukumar shari’ar ƙasar ta Holland sun ce sun samo sabbin hujjoji, waɗanda, bisa matakan tsananta dokokin yaƙi da ta’addanci a ƙasar da aka ɗauka, za su iya sa a yanke wa Samir Azzouz, haifaffen birnin Amsterdam, amma mai asali daga Marokko, hukunci. Tare da Samir Azzouz, mai shekaru 20 da haihuwa, ana kuma zargin wasu mutane 5 ne, a cikinsu har da wata mace, Soumaya Sahla, mai shekaru 23 da haihuwa da mijinta da waɗannan laifuffukan.
Jami’an ɗaukaka ƙarar jama’a sun faɗa wa kotun cewa, sun kame Azzouz da muƙarrabansa ne da miyagun makamai, da libarba, da albarusai da takardun bayanai kan yadda za a iya yin amfani da tarho na salula wajen ta da nakiya. Sun kuma ce Azzouz ya tuntuɓi wani mutum don ya taimake shi wajen kai harin ƙunan baƙin wake a kann hedkwatar ’yan sandan ciki na ƙasar Holland ɗin. A cikin wata mai zuwa ne dai ake sa ran kotun za ta yanke hukunci.