An fara shari'ar wani ɗan Ruwanda a Frankfurt
January 21, 2011Ko da yake har ila halin da ake ciki yanzu rikicin ƙasar tunesiya da sauran sassa na arewacin Afirka na ci gaba da ɗaukar hankalin jaridu da mujallun Jamus, amma a ɗaya ɓangaren sun ba da la'akari da ire-iren ci gaban da ake samu a sauran yankuna na Afirka. A cikin wani rahoton da ta bayar jaridar Frankfurter Rundschau ta yi bitar irin mummunan tasirin da manufofin noma na ƙasashen Turai ke yi akan ƙananan manoma a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce:
"Manoma na ƙasashen Turai su ne kawai ke cin gajiyar manufofin noma na ƙasashen nahiyar sakamakon dubban miliyoyin da ake kashewa don karya farashin amfanin da manoman ke samarwa. Domin kuwa wannan amfanin ba ana cinikinsu ne a ƙasashe maƙobta na Turai ba, ana fitar da su ne zuwa ƙasashe kamar su Cote d'Ivoire da ragowarsu. Ƙasar ta yammacin Afirka ta bunƙasa yawan amfanin da take sayowa daga ƙetare daga tan dubu biyar a shekara ta 2000 zuwa kimanin tan dubu talatin da biyar a shekara ta 2006. A sakamakon haka harkar noma ta cikin gida ta wargaje, inda aka samu koma bayan amfanin da manomanta ke samarwa daga tan dubu goma sha takwas zuwab tan dubu biyar kacal."
A wannan makon aka gabatar da wani ɗan ƙasar Ruwanda da aka daɗe ana nema ruwa a jallo, a gaban kuliya, a birnin Frankfurt bisa zarginsa da laifin kisan mutane sama da dubu uku a ta'asar kisan kiyashin da ta wanzu a ƙasar Ruwanda a shekarar 1994. Jaridar Der Freitag ta yi bitar lamarin tana mai cewar:
"Ko da yake ba wanda ya san tahaƙiƙanin tarihin rayuwar Onesphore mai hannu a kisan ƙare-dangi a Ruwanda, inda wasu ke iƙirarin cewar wai a Frankfurt ne yayi karatunsa na jami'a, amma fa a haƙiƙatal-amari a shekara ta 2002 ne, wato shekaru takwas bayan wanzuwar ta'asar ta kisan kiyashi a Ruwanda, Onesphore ya shigo Jamus don neman mafakar siyasa. An ba shi wannan dama, inda ya ci gaba da rayuwarsa tare da matarsa da 'ya'yansu guda uku. Ya shiga inuwar wata ƙungiya ta coci kuma babbar 'yarsa zata kammala sakandare nan ba da daɗewa ba. Amma fa a zamanin baya a matsayinsa na magajin garin Muvumbu, mai laifin ya taka muhimmiyar rawa wajen yi wa 'yan Tutsi kisan ƙare dangi."
China na daɗa faɗaɗa angizonta a ƙasashe masu tasowa a ƙoƙarinta na kare makomar ɗayyun kayayyakin da take buƙata daga waɗannan ƙasashe. Wannan dai shi ne kanun wani rahoton da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta ta kuma ƙara da cewar:
"Rikicin kuɗin da aka fuskanta ya zama tamkar faɗuwa ce ta zo daidai da zama ga ƙasar China domin ya share mata hanyar ƙara ƙarfafa dangantakar cinikinta da ƙasashe masu arziƙin ɗanyyun kayayyaki, inda take irin cinikin nan na ba ni gishiri in ba ka manda da waɗannan ƙasashe. A sakamakon ƙaƙƙarfan matsayin tattalin arziƙin da take da shi da isassun kuɗaɗen musaya na ƙetare Chinar ba ta ji raɗaɗin rikicin na kuɗi ba, inda a shekarar da ta wuce kamfanonin ƙasar suka zuba jarin da ya kai na kwatankwacin dalar Amirka miliyan dubu hamsin a ƙasashen ƙetare. Dangane da ƙasashe masu tasowa kuwa Chinar ta zama musu wata kyakkyawar mafaka domin kauce wa matsin lamban bankin duniya da ƙasashen yammaci."
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Umaru Aliyu