Afghanistan: Fara jigilar fararen hula
September 9, 2021Talla
Rahotanni sun nunar da cewa a yau Alhamis jirgin saman Qatar-Airways ya tashi da mutane sama da 200 zuwa Doha fadar gwamnatin Katar din. Cikin wadanda aka samu nasarar kwashewa a jirgin farkon, akwai 'yan kasashen Jamus da Amirka da Kanada da Birtaniya da Italiya da Holland da kuma Ukraine. Ana sa ran a Jumma'ar wannan makon, wani jirgin dauke da fararen hular 'yan kasashen waje zai sake tashi daga Afghanistan din. Jakadan musamman na Katar a Afghanistan din, Mutlak al-Kahtani ya bayyana cewa, filin jiragen saman na birnin Kabul ya koma aiki ka'in da na'in. Kasashen Katar da Turkiyya dai, na aiki kafada da kafada, domin ganin al'amura sun koma yadda suke a filin jiragen samana na birnin na Kabul.