An haramta shawagin jiragen sama a Zamfara
March 2, 2021A cigaba da kokarin neman mafitar rashin tsaron da ke dada kamari a cikin tarrayar Najeriya, majalisar tsaron kasar ta tsaida aiyukan hakar ma'adinai a Zamfara, ko bayan haramta shawagi na jirage a cikin yankin.
Majalisar da ta share kusan awoyi biyar tana wani taron sirri dai ta ce akwai alaka ta hakar ma'adinai da halin rashin tsaron da ke Zamfara.
Abujar da ta ce ta baiwa sojojin kasar umarnin mamaye dazuka na Zamfara, ta kuma sanar da tsaida aiyukan hakar ma'adinai cikin jihar har illa masha Allah.
Haka kuma majalisar a fadar Manjo Janar Babagana Monguno da ke zaman mashawarci na tsaro na kasar, ta haramta shawagi na jirage a daukacin jihar.
Tun bayan satar 'yan mata 'yan makarantar Jangebe da ke cikin jihar ta Zamfara dai hankulan daukacin kasar ya karkata ya zuwa sabuwar sana'ar satar 'yan makarantar da ke dada samun farin jini a tsakanin 'yan ina da kisan.
To sai dai kuma in har gwamnatin ta shirya sa kafar wando guda da barayin na Zamfara daga dukkan alamu kuma ta fara hararar wasu a cikin kasar da ta ce na neman wuce makadi da rawa cikin rikicin rashin tsaron.
Kuma a fadan mashawarcin, jami'an tsaron kasar na bin diddigi da nufin kaisu ga shari'a.
Duk da cewar dai gwamnatin kasar na buga kirjin cimma da dama ga batu na tattali na arziki da sake farfado da ababe na more rayuwa, batun tsaron dai na shirin zama bakin fentin da ke neman rusa daukacin cigaba na gwamnatin.
To sai dai kuma a fadar Senata Hadi Sirika da ke zaman daya a cikin ministoci na gwamnatin kasar, akwai kwakkwaran cigaba a tsakanin inda gwamnatin ta faro ya zuwa inda kasar take a halin yanzu.
Batun tsaron dai na zaman na farkon farin da ya kai karshen 'yan lema, ya kuma tabbatar da mulkin na tsintsiya a tarrayar Najeriyar. Kuma daga dukkan alamu batun tsaron ne ke neman kai karshen farin jini na tsintsiyar musamman ma a arewacin kasar dake zaman tunga ta magoya bayanta.