SiyasaJamus
An dage babban zaben Libiya
October 6, 2021Talla
A ranar 24 ga watan Disamban wannan shekara ne aka kayyade za a gudanar da zaben ‘yan majalisar da na sghugaban kasa, zaben da ke da matikar muhimmanci wajen kawo karshen yakin basasa da rudanin siyasar da Libiyar ta jima a ciki tana fama da su.
Tun da jimawa, bangarorin biyu masu karfin fada a jin a fagen siyasar Libiya wato majalisar dokokin da ke Toubrouk a gabashin kasar da ta majalisar koli da ke gudanar da sha'anin mulkin da ke da matsayin majalisar dattikjai mai da mazauni a birnin Tripoli, ke samun mabanbantan ra'ayi kan batun tsara zaben gama gari.