1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekaru biyar da kama Gbagbo

Tilla AmadouApril 11, 2016

Ana zargin tsohon shugaba Laurent Gbagbo na Cote d'Ivoire da yanzu haka yake fuskantar shari'a a kotun duniya ta ICC da ke The Hague da laifukun take hakkin jama'a.

https://p.dw.com/p/1ITLN
Elfenbeinküste Präsident Laurent Gbagbo
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kooren

Ana zargin cewar da gangan magoya bayan Gbagbo suka kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar. Mutane dai kusan dubu uku ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar tashin hankalin da aka shafe watanni ana yi.

To ko yaya al'ummar kasar ta Cote d'Ivoire ke ji dangance da zagayowar wannan rana? Yabe Kone malamin makaranta ne a Abidjan baban birnin kasar :

"Shekaru biyar da su ka wuce, mun wahala sosai musamman ma in kana musulmi, wata rana saboda shi aka kusa kasheni da amma yau komai ya wuce, kana zuwa inda ka so cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba, kuma kasar mu komai na tafiya lafiya musumman yada tattalin arziki kasar mu ya bunkasa."

Kotun duniya mai hukunta miyagun laifuffuka ta ICC ta ce tsohon shugaban Cote d' Ivoire Laurent Gbagbo ya na fuskantar tuhuma bisa aikata laifuffuka hudu na cin zarafin bil Adama da suka hada da kisa da kuma fyade. Duk da cewa har yanzu akwai magoya bayanshi da suka ki amincewa da wannan tuhuma.