1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto jirgin 'yan cirani

Abdourahamane Hassane
December 22, 2018

Wata kungiya mai aiki agaji ta Open Arm ta Spain ta ceto 'yan cirani kusan 300 da jirgin ruwanta a gabar tekun Libiya.

https://p.dw.com/p/3AXyu
Spanien Mehr als 300 Migranten im Mittelmeer gerettet
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Calvo

Shugaban kungiyar Oscar Camps ya bayana a shafinsa na Twitter cewar mutanen da suka ceto sun hada da maza da mata da yara kanana har ma da mata masu juna biyu da jarirai. Sai dai a halin da ake ciki hukumomin Italiya sun ki amincewa da karbar jingin ruwan. Tun da farko jirgin ruwan ya doshi kasar Malta ne amma kuma hukumomin kasar suma suka ki karbarsa.