Ceto bakin-haure a Libiya
July 12, 2019Talla
Masu gadin gabar tekun Libiya sun bayyana kama wani jirgin ruwa dauke da bakin-haure fiye da 20 masu neman tsallaka teku domin shiga kasashen Turai. Kofofin yada labaran kasar ta Libiya sun ce bakin-haure sun fito daga kasashen Masar, da Sudan, gami da Libiya.
A cikin wata sanarwa hukumomin sun bayyana mika mutane ga masu aikin jinkai gami da taimakon lafiya, inda aka kai su wani sasansanin 'yan gudun hijira.