An cafke fiye da mutane 100 a Kamaru
November 23, 2016Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa fiye da mutane 100 aka kama yayin da mutum daya ya gamu da ajalinsa sakamakon kwanaki uku da aka kwashe dubban mutane suna zanga-zanga cikin yankin kasar da ake magana da harshen Turancin Ingilishi. Akwai masu zanga-zanga kimanin 10 da suka samu raunika daga harbin jami'an tsaro kamar yadda daya daga cikin shugabannin da suka shirya zanga-zangar ya shaida wa kamgfanin dillancin labaran Jamus na DPA.
Zanga-zangar da ke gudana a garin Bamenda da ke zama helkwatar Lardin Arewa maso Yamma ana nuna takaici bisa wariyar da gwamnatin Kamaru ke yi ga masu magana da harshen Ingilishi a kasar da galibi ake magana da Faransanci. Masu zanga-zanga suna zargin yankin da rashin samun kudaden da ake bukata wajen gudanar da harkokin yau da kullum idan aka kwatanta da sauran bangarori na kasar.