1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kawo karshen yakin Libiya

October 5, 2020

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya nemi ganin an kawo karshen yakin basasa da ya tagaiyara kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3jTIE
Libyen | Truppen von General Chalifa Haftar
Hoto: Esam Omran Al-Fetori/Reuters

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci manya kasashen duniya da ke da su karfi da karfe wajen ganin an tsagaita wuta a yakin basasar kasar Libiya, sakataren ya jaddada cewa makomar kasar ta Libiya na cikin hatsari.

Majalisar ta Dinkin Duniya hadin gwuiwa da kasar Jamus sun shirya wani taro na wuni daya domin lalubo bakin zaren rikicin na Libiya, inda aka tattauna batun yadda bangarorin da basu ga maciji da juna gami da 'yan koransu suka yi fatali da takunkumin shigowa da makamai a kasar.

Kasar ta Libiya dai ta tsunduma cikin rikici ne bayan da wani yunkurin da ya samu goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO ya hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gadhafi.