An bude wasanni olympics na lokacin sanyi a Turin na Italiya
February 11, 2006Talla
Tare da wani kasaitaccen buki an bude wasannin olympics na lokacin sanyin hunturu karo na 20 a birnin Turin dake kasar Italiya. ´Yan wasan tsalle-tsalle da guje guje kimanin dubu 2 da 600 daga kasashe 82 zasu kwashe makonni biyu suna gwagwarmaya cin lambobi dabam dabam. An kiyasce cewa mutane sama da miliyan dubu 2 daga ko-ina cikin duniya zasu kalli wasannin olympics din ta akwatunan telebijin. Tun dai ba´a kai ko-ina ba an fara fuskantar cece-kuce a wasannin. A halin da ake ciki an dakatar da ´yan tsere kan kankara su 12 har tsaawon kwanaki 5 bayan an gano kwayoyin halittu fiye da kima a cikin jininsu. An kuma hana wani fitaccen dan tsere akan kankara na Amirka Zach Lund shiga wasannin na bana sannan an hana shi shiga duk wani wasa har tsawon shekara guda bayan ya fadi a gwajin magunguna kara kuzari.