An bude sabon babi a rikicin Iran da Isra'ila
April 13, 2024Shugaba Joe Biden na Amurka ya yanke hutunsa na karshen mako domin gudanar da taron gaggawa da mashawartansa kan harkokin tsaro a fadar White House, sa'o'i kadan bayan da Iran ta kama wani jirgin ruwa mallakin Isra'ila a kabar takun Gulf a ranar Asabar 13.04.2024.
Karin bayani: Sojojin Iran sun kama wani jirgin ruwan kasar Isra'ila a gabar ruwan Gulf
Sai dai fadar mulki ta White House ba ta sanar da cewa ba ko da akwai wani matakin gaggawa da Amurka za ta dauka kan wannan al'amari da ke zuwa a daidai lokacin da ake cikin fargabar rincabewar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya da ke kara daukar dumi, bayan da Iran ta sha alwashin kai wa Isra'ila harin ramuwar gayya a matsayin martani ga harin ta kai wa ofishin jakadancinta da ke birnin Damaskas na Siriya a ranar daya ga watan Afrilu.
Karin bayani: Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran na IRNA ya ce tuni sojojin kasar suka karkata akalar wannan jirgin zuwa yankinsu daga gabar tekun Gulf mai matukar muhimmanci ga kasuwancin duniya.
Hukumomin da ke kula da tsaro da kuma sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwan 'yan kasuwa a yankin Gulf sun ce dakarun juyin juya halin Iran sun yi amfani da jirgi mai sukar ungulu wajen dira a kan jirgin ruwan na Isra'ila kafin daga bisani su karkata akalarsa.