Daruruwan mutane sun halarci zana'idar Pervez
February 7, 2023Talla
A wannan Talata an binne tsohon shugaban kasar Pakistan Marijayi Janar Pervez Musharrafa a birnin Karachi mai tashar jiragen ruwa na kudancin kasar inda iyalansa suke, bayan wani jirgin na musamman da aka yi shata ya dauko gawar marigayin daga birnin Dubai na Hadaddiyar Daulan Larabawa inda ya rasu a karshen mako.
Kimanin mutane 2,500 da suka hada da iyalan marigayin da 'yan uwa da abokan arziki gami da 'yan siyasa suka halarci zana'idar da aka yi masa. Kafin binne shi a makabartar barikin soja da ke birnin na Karachi.
Shi dai Marigayi Janar Pervez Musharraf ya bar duniya yana da shekaru 79 da haihuwa kuma ya mulki kasra ta Pakistan daga 1999 lokacin da ya kwace madafun iko a wani juyin mulkin soja ya yi mulki har zuwa shekara ta 2008.