An bai wa Orhan Pamuk lambar girmamawa ta zaman lafiya a birnin Frankfurt.
October 24, 2005Kololuwar taron baje kolin litattafai da ake yi a ko wace shekara a birnin Frankfurt dai, ita ce bikin mika lambar girmamawan nan ta zaman lafiya, wadda kuma ta kunshi kyauutar kudi na Euro dubu 25, da kungiyar `yan kasuwan litattafai ta nan Jamus ke bayarwa. Bisa al’adar da masu shirya taron ke bi dai, ana ba da wannan kyautar ne ga marubuta da suka bajinta a cikin rubuce-rubucensu, wadda a ganin kwamitin ba da kyautar, ke taimakawa wajen samad da zaman lafiya tsakanin al’ummomi a yankuna daban-daban na duniya.
Orhan Pamuk, wani marubuci daga kasar Turkiyya ne ya sami lambar girmamawan ta wannan shekarar. A bikin mika masa kyautar da aka gudanar a cocin Paulus da ke nan birnin Frankfurt, jiya lahadi, kusan manyan baki dubu da aka gayyata ne suka halarci shagalin.
An haifi Orhan Pamuk ne a ran 7 ga watan Yuni a shekarar 1952 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya. Ya yi karatun tsarin gine-gine da na aikin jarida, kafin ya shiga rubuce-rubuce. A halin yanzu dai, yana daya daga cikin shahararrun marubutan kasarsa, wadanda suka dukufad da ayyukansu kan batutuwan da suka shafi adabi na wannan zamanin. An fasara ayyukansa zuwa fiye da harsuna 34, kuma, an buga litattafansa a cikin fiye da kasashe 100 na duniya. Ban da dai wannan kyautar, Orhan Pamuk, ya sami kuma wasu kyaututtuka, tun da ya fara buga farkon litattafansa guda biyu a cikin shekarar 1982 da kuma 83.
A cikin jawabinsa na karbar kyautar, Orhan Pamuk ya nanata cewa:-
„ A wannan zamanin da muke ciki, al’ummomi na addinai, ko na kabilu, ko na kasashe, suna kara samun wayewar kai ne da fahimtar kansu ne ta hanyar adabi ko litattafan da aka wallafa. Ta hakan ne kuma suke iya tattauna batuttuwan da suka fi addabarsu. Yayin karanta wani littafi don shakatawa ne muke shiga cikin wani hali, wanda ke sanya mu cikin zurfin tunani kan al’umman da muke ciki, ko kasarmu ko ma rayuwa gaba daya.“
Pamuk dai, ya yi kira ga marubutan kasarsa, da su fito fili su dinga bayyana halin da kabilu `yan tsiraru, kamar Kurdawa ke ciki a Turkiyyan. Ya kara da cewa:-
„Cikas ne ga wani marubuci na nan Jamus, ya yi bayanai kan halin rayuwa na yau da kullum a kasarsa ba tare da ambatar Turkawan da suka yi kaka gida a wannan kasa ba. Kazalika kuma, ina ganin cewa, wani babban cikas ga duk wani marubucin Turkiyya na wannan zamanin, idan ya ki takalo batun Kurdawa, da `yan tsiraru, da kuma wasu batutuwan tarihi da har ila yau ke cikin duhu, a cikin rubuce-rubucensa.“
Tun 1950 ne dai, kungiyar Kasuwancin litattafai ta nan Jamus ta fara ba da wannan kyautar, a lokacin taron baje kolin litattafai na birnin Farnkfurt. A cikin manyan bakin da suka halarci bikin ba da kyautar jiya a cocin Paulus da ke birnin Farnkfurt har da shugaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, Norbert Lammert, da ministan harkokin cikin gida mai jiran gado, Wolfgang Schäuble, da ministan kudi na tarayya Hans Eichel.