1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amurka ta kakaba takunkumai a kan kamfanonin Sudan

January 31, 2024

Amurka ta kakaba sabbin takunkumai a kan wasu cibiyoyin kasuwanci uku a kasar Sudan, cibiyoyin da ta hakikance cewa suna da alaka da bangarorin da ke yaki da juna tun a bara.

https://p.dw.com/p/4btyl
Wani yanki na birnin Khartum a Sudan
Wani yanki na birnin Khartum a SudanHoto: Ute Grabowsky/photothek/picture alliance

Wannan na daga cikin jerin matakan da Amurkar ta bijiro da su a kan Sudan din musamman, da nufin dakile yakin da ake cikin wata na tara ana gwabzawa.

Wadanda Amurkar ta kakaba wa takukuman dai sun hada da bankin Alkhaleej da Al-Fakher Advanced Works wadanda ke karkashin ikon rundunar ko ta kwana ta RSF.

Akwai ma Zadna International da rundunar sojin gwamnati ke kula da shi aewar ma'aikatar kula da harkokin Baitul Malin Amurka.

Dukkanin kamfanonin hada-hadar kudaden dai a cewar Amurkar suna taimaka wa bangarorin da ke daukar nauyinsu da kudaden da ke kara ta'azzara yakin da kasar ke a ciki.