1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amurka ta bukaci masu yaki a Sudan su daina cin zarafi

August 27, 2024

Rahotanni sun bayyana cewa dukkan bangarorin da ke yaki a Sudan sun rika cin zarafin mutane musamman mata da yara.

https://p.dw.com/p/4jyve
Mohamed Hamdan Daglo
Mohamed Hamdan DagloHoto: Ashraf Shazly/AFP

Wani babban jami'in Amurka ya bukaci bangarorin da ke yaki da juna a Sudan su daina cin zarafin al'umma kamar yadda ake gani a halin yanzu a cikin kasar.

Tom Perriello ya ce sojin Sudan na bitar daftarin kawo karshen yakin a yayin da bangaren mayakan sa kai na RSF suka sanya hannu kansa.

Bukatar isar da agajin gagawa a Sudan

A wannan watan na Agustan 2023 ne mayakan RSF suka amince da batun guje wa cin zarafi bayan Amurka ta shirya wata tattaunawa a birnin Geneva na Switzerland da zummar kawo karshen yakin da ya fi daidaita mutane a duniya.

Cutar kwalara ta sake kunno kai a Sudan mai fama da yaki

Mai shiga tsakani daga kasar ta Amurka a yakin na Sudan Tom Perriello ya kara da cewa Amurka ta gabatar wa bangaren sojinSudan daftarin daina cin zarafi kuma tana jiran amsa, bayan bangaren sojin ya ki bayyana a tattaunawar da aka gudanar a Switzerland.