1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amnesty:EU nada hannun a tauye hakkin 'yan gudun hijira

Ramatu Garba Baba
September 24, 2020

Kungiyar Amnesty International ta ce ba a san inda aka yi da dubban bakin hauren da 'yan tawaye suka kwashe daga wani sansani da aka kebe don tsugunar dasu a yayin da suke yunkurin shiga Turai ta Libiya ba.

https://p.dw.com/p/3ivRk
Amnesty International - Symbolbild
Hoto: Getty Images/G. v.d. Hassel

A wani rahoto da ta fitar a wannan Alhamis, Kungiyar Amnesty International ta ce dubban 'yan gudun hijira da ake tsare da su a wasu sansanoni a Libya sun yi batan dabo. Rahoton ya ci gaba da cewa, wadanda suka batan, na daga cikin dubban da aka tsugunar a sansanonin da 'yan tawaye da ke biyayya ga gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Amnesty ta daura alhakin kuncin da 'yan gudun hijira suka sami kansu kan Kungiyar tarayyar Turai da ta dauki matakin rufe iyakokinta da sunan yakar annobar Corona ba tare da duba halin da za su kasance ba. 

'Yan gudun hijira daga Afrika sun dade suna bi ta cikin Libiya domin ketarawa zuwa Kudancin nahiyar Turai, sai dai bayan gano irin azabar da ake ganawa da dama daga cikinsu a wasu sansanonin tsare bakin hauren, kasashen duniya suka sha alwashin magance matsalar ba tare da yin nasara ba.