1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar fyade na karuwa a Najeriya

Ramatu Garba Baba
November 17, 2021

Amnesty International ta bankado yadda ake samun karuwar matsalar fyade a Najeriya ba tare da mahukunta na daukar matakin hukunta masu aikata laifin ba.

https://p.dw.com/p/437sR
Nigeria | Protest nach Vergewaltitung
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce, a Najeriya, an samu karuwar matsalar fyade da kuma rashin yi wa matan da aka yi wa fyaden adalci, koda kuwa sun yi kokari sun shigar da kara a gaban kotu.

Kungiyar mai kare hakkin bil Adama ta ce, akwai daruruwan matan da aka yi ma fyade da ba a san takaimaimen yawansu ba, saboda da dama daga cikinsu sun gwanmace yin gum da bakinsu don gudun tsangwama koma a karyatasu.

A wani rahoto na UNICEF na can baya, ya nuna cewa, akalla daya daga cikin mata hudu a Najeriya ake yi wa fyade kafin ta cika shekara goma sha takwas da haihuwa. Kawo yanzu gwamnatin Najeriyar ba ta mayar da martani kan wannan sabon rahoton na Amnesty da ta fitar a wannan Laraban ba.