Amirka za ta kwashe jama'arta da ke Nijar
August 3, 2023Talla
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amirka ta ce, ta fara shirin kwashe ma'aikatanta da ba su yin aikin kai daukin agajin gaggawa da kuma iyalan da suke offishin jakadancinta da ke birnin Yammai.
Kakakin ma'aikatar, Matthew Miller ya ce, offishin zai kasance a bude domin gudanar da wasu ayyukan gaggawa da za su iya tasowa. Tuni dai gwamnatin Washington ta shawarci Amirkawa da su kaurace wa yin balaguro zuwa Nijar.
A makon da ya gabata ne sojoji suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, inda suka kifar da gwamnatin farar hula ta shugaba Mohamed Bazoum.