Amirka ta yaba wa jagoran yakin Libiya
April 20, 2019Talla
White House din ta ce tattaunawar wacce a cikinta Shugaba Trump ya yaba wa madugun yakin na Libiya, na daga cikin tsayuwar da Amirka na ganin an yaki ta'addanci da ma kare albarkatun man kasar.
To, sai dai masu kallon al'amura na fassara ganawar ta Juma'a, musamman yaba wa Haftar da Trump din ya yi, a matsayin taimaka masa ne a gwagwarmayar da yake yi don kwace iko a Libiyar.
Tattaunawar ta zo ne yayin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke fadi-tashin ganin an tsagaita wuta.