1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kai wa dakarun IS na Iraki farmaki

August 8, 2014

Sojin Amirka sun kai farmaki Iraki da jirgin yaki kan 'yan kungiyar IS da ke fafutukar kafa daular Musulunci a kasar da sauran yankunan da ke makotaka da ita.

https://p.dw.com/p/1CreF
F/A-18 Super Hornet US-Kampfjet USA Irak Islamischer Staat Symbolbild Angriff
Hoto: picture-alliance/dpa

Amirkan dai ta kai harin ne bayan da 'yan kungiyar ta IS suka kai hari kan dakarun Kurdawa da ke kokarin kare kansu da kuma babban birnin yankinsu wato Irbil.

Baya ga harin da sojin na Amirka suka kai, wani jami'an ma'aikatar tsaron kasar ya ce sun jefawa dubban 'yan Iraki da ke cikin tsananin bukata kayan abinci da kuma ruwan sha.

Tuni da kawayen Amirka musamman ma dai Birtaniya suka yi na'am da wannan mataki da Amirkan ta dauka wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da Shugaba Barack Obama ya fara janye dakarun Amirkan daga Iraki a shekara ta 2011.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal