Amirka ta fidda matsaya tsakaninta da China
March 20, 2019Talla
Kalaman Shugaba Donald Trump na Amirka a wannan Laraba, ga dukkan alamu sun mayar da hannun agogo baya a tunanin da ake yi na cewar matsalar cinikayya tsakanin kasashen na iya sauyawa.
A makon gobe ne jami'an Amirka da na China za su gana a birnin Beijing.
Mr. Trump ya ce za su cimma yarjejeniyar cinikayyar ne kawai, muddin suka tabbatar da cewa Chinar za ta cika alkawuran da za su amince a kansu.
Amirka dai na da bukatar wasu sauye-sauye ne daga tsare-tsaren cinikayyar kasar China.