Amirka ta dakatar da gabilin taimakon Gabon
September 27, 2023Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta kasar Amirka ta dakatar da gabilin taimakon da bai shafi jinkai ba ga kasar Gabon sakamakon juyin mukliin da sojoji suka yi a watan jiya na Agusta wanda ke zama juyin mulki na biyu a nahiyar Afrika cikin wannan shekara.
Sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka, Antony Blinken ya bayyana dakatar da taimakon kan kasar ta Gabon har zuwa lokacin da aka sauyin da aka samu bayan juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin tsohon Shugaba Ali Bongo, amma gwamnatin Amirka ta ce matakin ba zai shafin ayyukanta a kasar ta Gabon mai arzikin man fetur na yankin tsakiyar Afirka ba.
Haka kuma gwmnatin ta Amirka ta katse wasu ayyukan taimako a Jamhuriyar Nijar samakaon kwace madafun iko d asojoji suka yi a kasar da ke yankin yammmaci9n Afirka, aamma a hukunce gwamnaatin ta Amirka ba ta ayyana abin da ya faru a Jamhuriyar Nijar a matsayin juyin mulki ba.