Amirka: Majalisa ta tabbatar da zaben Joe Biden
January 7, 2021Talla
Bayan zaman da suka yi na hadin gwiwa, majalisun dokokin Amirka sun amince da nadarar da Joe Biden ya samu a zaben shugaban kasa da ya gudana a watan Nuwamban bara.
Tun da fari dai zaman na majalisun ya hadu da tarnakin magoya bayan shugaba Donald Trump da ya sha kayi a zaben, kafin daga bisani bayan sa'o'i kalilan a cigaba da shi.
Majalisar Dinkin Duniya gami da kasashen da ke fada a ji a fadin duniya da suka hada da China da Jamus, suka bayyana abin da ya faru a matsayin karan tsaye ga demokaradiyya.