1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump da Biden sun caccaki juna

Ramatu Garba Baba
September 30, 2020

Kusan fada aka yi a karon farko a tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar Amirka Donald Trump da Joe Biden a yayin gudanar da muhawara kamar yadda aka saba yi a tsakanin manyan 'yan takarar kujerar shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3jCUh
USA Präsidentschaftswahlen TV Debatte Trump Biden
Hoto: Jonathan Ernst/Reuters

A Amirka an kwashi mintuna casain ana tafka muhawara a tsakanin 'yan takarar kujerar shugabanci na manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu, wannan shi ne karon farko da Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican ke fuskantar juna da abokin hamayyarsa Joe Biden na jam'iyyar Demokrat.

Muhawarar ta kasance tamkar fada ganin yadda 'yan takarar biyu suka yi ta jifan juna da munanan kalamai, masu sharhi na ganin sun saki layi inda suka kauce daga baiyana manufofinsu kan ayyukan raya kasa.

Jama'a da dama na son jin yadda kowannensu zai tunkari matsaloli in har yai nasara a game da tsarin inshorar lafiya da matsalar dumamar yanayi da sauransu. Muna tafe da karin bayani kan wannan batu a jerin rahotannin shirin bayan labaran duniya.