Kanada za ta tattauna batun kasuwanci da Amirka
August 28, 2018Talla
Hakan na zuwa ne bayan da Amirkan ta sanar da rattaba hannu tare da kasar Mexiko kan wannan yarjejeniya a wani mataki na neman dawo da yarjejeniyar kasuwanci da ke tsakanin kasar ta Amirka da kasashen yankin arewacin Amirka.
Shugabar diflomasiyyar kasar ta Kanada Freeland, wadda nauyin cimma wannan yarjejeniya ya rataya a kanta ta katse wata ziyara da ta ke yi a Tarayyar Turai domin zuwa kasar ta Amirka wajen wannan tattaunawa bayan da fadar shugaban na Amirka ta sanar cewa Amirka da Mexiko sun cimma yarjejeniyar.
A baya dai shugaban na Amirka Donald Trump ya zargi wannan yarjejeniya tsakanin Amirka da kasashen na Arewacin Amirka wajen gurbata dubban ayyuka na 'yan kasar ta Amirka.