Democrats ta doke Republicans a Georgia
January 6, 2021Tuni dai aka ayyana cewa, dantakara Raphael Warnock ya yi galaba a kan Sanata Kelly Leoffler yayin da shi kuma John Ossob ya ayyana cewar ya samu nasara a kan abokin hamayyarsa sanata mai ci David Perdue. Du da cewa a hukumance ba a bayyana sakamakon zaben na John Ossob da David Perdee ba, amma Ossob ne a kan gaba a kusan kaso 99 cikin 100 na kuri'un da aka kidaya.
Karin Bayani: Trump ya ce shi yai nasara a zaben Amirka
Cikin jawabin da Warnock ya yi jim kadan bayan da ya lashe zaben, ya nuna cewa ya tabbatar a siyasar Amirka komai na iya faruwa kuma kasa ce da ke bai wa kowa dama, musamman idan aka duba tarihin yadda ya tashi cikin wahala. Ya kara da cewa shi ba dan kowa ba, amma yau ga shi zai wakilici babbar jiha kamar Georgia: "Zan ta fi majalisar Dattawa domin in yi wa dukkan al'umar Gerogia aiki ba tare da la'akari da wanda suka kadawa kuri'a ba, a wannan lokaci mai cike da tarihi a Amirka.
Warnock ya kafa tarihi, a matsayin zababben sanata bakar fata na farko daga Georgia, jihar da tun kusan fiye da shekaru 20 da suka wuce, take hannun 'yan jam'iyyar Republican. Shi ma da yake yin tsokaci, tsohon gwamnan jihar Ohio John Kesich wanda ya ce shi cikakken dan jam'iyar Republican ne, amma rarrabuwar da jam'iyyar take yi da fadan cikin gida da yadda Trump yake sabauta jam'iyar ne suka sa aka kada su a jihar Georgia: "Sun shiga rudu. Abin takaici ne sosai. Ina fatan za mu koyi darasi domin a tunkari gaba."
Karin Bayani: Shugabanin kasashen duniya na taya Joe Biden murna
Za a iya alakanta wannan nasara da Demokrats ta yi da wasu manyan dalilai, daga ciki akwai kallon sakamon a matsayin babban sako da 'yan Georgia suka sake aikewa Shugaba Trump mai barin gado cewa sun dawo daga rakiyarsa, kamar yadda suka kada shi a zaben da aka kammala cikin watan Nuwamba. Haka zalika, kokarin da Jagorar Demokrats a jihar Bakar Fata Stacey Abraham ta yi wajen ci gaba da wayar da kan jama'a musanman bakar fata cewa, su fito su bayar da kuri'unsu, shi ma ya taimaka.
Karin Bayani:Joe Biden na yunkurin hada kan Amirkawa
Akwai kuma 'yan Republican da suka juyawa jam'iyyarsu baya, domin nuna fushinsu da yadda Shugaba Trump ya dage sai ya sauya sakamakon zaben da aka yi a jihar. A halin da ake ciki dai, nan da wani lokaci a wannan Larabar, wani zaman hadin-giwa na majalisun Amirkan biyu zai kada kuri'ar tabbatar da nasarar da Joe Biden ya yi a matsayin shugaban kasa mai jiran gado, makwanni biyu kafin yayi rantsuwar kama aiki.