1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya tana cikin matsalar ambaliyar ruwa

October 12, 2022

A yayin da ake ci gaba da sheka ruwan sama a sassan Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ambaliyar da ake gani cikin kasar na zaman mafi girma a cikin sama da shekaru 10.

https://p.dw.com/p/4I6DZ
Najeriya I Ambaliyar ruwa a jihar Kogi
Najeriya ambaliyar ruwaHoto: Fatai Campbell/AP/picture alliance

 

A mafi yawan na kauyuka da birane da kwale-kwale ya maye gurbin kekuna da babura da motoci a matsayin hanyoyin sufuri. Kuma manya da kananan tituna mallakin gwamnatin tarraya da jihohi da sun karye ko bayan gadojin da ke barazanar raba sassan arewacin kasar da kudancinta.

Karin Bayani: Daminar bana mai cike da ambaliya

Flut Nigeria Afrika 2010 Flash-Galerie
Ambaliyar ruwa a NajeriyaHoto: AP

Wata kiddidigar gwamnatin tarraya dai ta ce mutane 500 ne suka rasu a yayin kuma da sama da mutane Miliyan daya dai ambaliyar ta kai ga rabawa da gidajensu. Sama da gidaje dubu 45,000 ne dai suka rushe, kana samada kadada 75,000 na gonaki ambaliyar ruwan ta lalata, barna mafi muni cikin kasar a shekaru da dama da suka gabata.

Sakin ruwa daga madatsar ruwan Lagdo a Kamaru dai ake ta'allakawa da sabuwar ambaliyar da ke kara tayar da hankalin nutane a yankin tsakiyar Najeriya. Tituna da gadoji na gwamnatin tarraya da jihohi dai sun rushe, kuma tuni Abujar a fadar ministan aiyyukan kasar Tunde Fashola ta fara kirga asarar ambaliyar ga harkar sufurin mai tasiri.

Afirka Najeriya ambaliyar ruwa
Najeriya ambaliyar ruwaHoto: AP

Dubban daruruwan mutane da ruwan ya raba da muhalli dai sun koma makarantu, abin da ya tilasta tsayar da karatu a sassan kasar a halin yanzu. Wasu a cikin jihohi na kasar ma dai na neman aiyana dokar ta-baci da nufin agazawa mutanen. Garba Shehu dai na zaman kakaki na gwamnatin tarrayar da kuma ya ce Abuja ta yi nisa a kokari na rage radadin barnar.