Mutane fiye da 100 sun hallaka sakamakon ambaliyar ruwa
July 15, 2019Talla
Alkalumman wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a wasu yankuna na kasashen Indiya da Nepal da kuma Bangladesh sun haura mutum dari. Ko baya ga asarar rayukan da ta haddasa, ambaliyar ta kuma tilastawa miliyoyin mutane barin matsuguninsu.
Yankin Assam da Bihar na Indiya na daga cikin yankunan da wannan ibtila'in ya afkamawa, a cewar wani rahoto da gwamnatin kasar ta fitar sama da kwanaki goma da suka gabata yankin na Assam ke fama da wannan ambaliyar ruwan.