1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Mutane 25 ambaliyar ruwa ta halaka a Indiya

Abdoulaye Mamane Amadou SB
October 17, 2021

Sojoji da jami'an agaji na kokarin ceton jama'ar da suka makale a sakamakon ambaliyar ruwa gami da zabtarewar kasa da suka halaka kimanin mutane 25 a kasar Indiya.

https://p.dw.com/p/41n5z
Indien Kerala | Überschwemmungen und Erdrutsche durch heftige Regenfälle
Hoto: APPU S. NARAYANAN/AFP//Getty Images

Hukumomi a Indiya sun ce kimanin mutane 25 suka halaka sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa. Lamarin ya auku a jihar Kerala da ke kudu maso yammacin Indiya, inda rahotanni ke cewa yanzu hakan sojoji da jami'an agajin gaggawa na ci gaba da ceton mutanen da lamarin ya shafa.

Tuni ma dai aka kafa sansanonin karbar mutane da hatsarin ya rutsa da su, a cewar gwamnan yankin a yayin da yake magana da manema labarai.

Wasu hotunan da suka karade shafukan sada zumunta, na nuna irin yadda ruwan ya mamaye motocin sufuri na mutane a yankin, kana tuni ma dai  Firaministan kasar ta Indiya Narendra Modi ya nuna alhini da ta'aziya kan wadanda suka rasa rayukansu a wani sakon da ya aike ta shafinsa na Twitter, tare da da bayyana cewa hukumomi za su kawo dauki ga wadanda abin ya shafa.