Ambaliya ruwa ta halaka mutane a Asiya
August 3, 2015Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ta shatatawa a 'yan makonni baya-bayan nan a Nahiyar Asiya sun yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane musamman a kasashen Indiya da Pakistan da kuma Bama.
Hukumomin Indiya sun bada sanarwar mutuwar mutane sama da 120 a kasar a yayinda wasu 116 suka halaka a kasar Pakistan. A kasar Bama ruwan saman sun haddasa zaftarewar kasa da ambaliya da ta lalata dubunnan gidaje da gonakki ,Gadoji dama hanyoyi.
Majalissar Dinkin Duniya ta ce ta damu kwarai da halin da ake ciki a yankin musamman a kasar Bama inda har kawo yanzu masu ayyukan ceto suka kasa isa garuruwa da dama da ruwan ya raba da sauran yankunan kasar musamman Jihar Rhakine inda mutane sama da dubu 140 suka samu mafaka a 'yan kwanakin bayan nan akasarinsu mambobin al'ummar tsirarun musulmin kasar 'yan kabilar Rohingyas.